Labarai
Afenifere:ta yi kira da a aiwatar da zabe ta na’urar mai kwakwalwa a zaben shekara ta 2023
Kungiyar yarabawa zallah ta Afenifere ta yi kira da a aiwatar da zabe ta na’urar mai kwakwalawa da kuma sake yin rijisstar zabe sabo, a yayin babban zabe da za’a yi a shekara ta 2023.
Wannan na kunshe cikin sanarwar bayan taro na bana da Kungiyar ta fitar da aka yi a fadar gwamnatin jihar Ekiti cewa, ta bukaci da ajanye katin zabe da ake amfani da shi a halin yanzu kafin a fara shirin sake sababbi a babban zaben da za’a mai zuwa.
Haka zalika kungiyar ta Afenifere ta ce zata cigaba da rajin sake sauya fasalin Najeriya ba tare da wani son zuciya ba.
Rahotanni sun bayyana cewar an karantawa manema labarai sanarwar bayan taron ne bayan da kungiyar ta kammala taron na yini biyu da yammacin jiya Lahadi
Da yake jawabin babban sakataren kungiyar na kasa Mr Kunle Famoriyo ya ce kungiyar ta yi imanin dukkanin sassan kasar nan zai amfana da sauya fasalin kasar nan, duk da bambanci al’adu da addini da kuma harshi.
Yayin da kungiyar ta yi kira ga gwamnatocin Kudu masu gabashin kasar nan da su samar da manofofi da zai daukaka al’adun kungiyar ta Afenifere da kuma bunkasa tatalin arzikin yankin.