Connect with us

Labarai

Ana gudanar da zaben cike gurbi a jihar Adamawa

Published

on

A yayin da aka fara gudanar da zaben cike gurbi a jihar Adamawa a yau, matainakin babban sifeton yan sandan kasar nan daga shiyya ta uku AIG Haruna Huzi Mrshalia ne ke jagorantar al’amuran tsaro a jihar.

 

Zaben dai zai gudana ne tsakanin yan takara biyu da suka hadar da gwamnan jihar Jibrila Bindow na jam’iyyar APC da kuma Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP

 

Ko da yake a baya jam’iyyar APC ta yi barazanar kauracewa shiga zaben, sai dai a yammacin jiya ne kuma suka lashe aman su suka kuma amince da shiga zaben.

 

A yanzu haka dai an girke jami’an tsaro a ko ina a fadin jihar karkashin mataimakin sifeton yan sadan kasar Haruna Huzi domin tabbatar da tsaro yayin gudanar da zaben.

 

Hukumar zaben ta kasa INEC ce dai ta ayyana zaben jihar a matsayin wanda bai kammala ba bayan da aka samu tazarar kuri’u40, 988 inda aka samu matsaloli a rumfunan zaben 44 a cikn mazabu 28

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 341,030 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!