Labaran Wasanni
Ahlan Cup: Kano Pillars ta lashe gasar ta 2021

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta kano Pillars ta lashe gasar cin kofin shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Jihar Kano mai taken Ahlan Cup.
An buga wasan dai a ranar Labara 10 ga watan Nuwamba 2021 a filin wasa na Ahmad Mu’azu dake sabuwar jami’ar Bayero dake jihar Kano.
Kano Pillars ta doke ƙungiyar kwallon kafa ta Doma United data fito daga jihar Gombe da ci 3-1 a wasan.
Doma United ce dai ta kare a matsayi ta 2 cikin ƙungiyoyi 12 da suka fafata a gasar.
Yayin da ƙungiyar kwallon kafa ta Elkenemi warriors dake mai Maidugurin jihar Borno ta ƙare a matsayin ta 3 a gasar.
A jawabinsa ƙyaftin din ƙungiyar Kano Pillars Rabiu Ali ya bayyana Godiyar sa ga Allah bisa samun nasara a gasar.
You must be logged in to post a comment Login