Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Nan bada jimawaba za a kammala aikin gyaran filin wasa na Sani Abacha dana Sabon Gari – Lakwaya

Published

on

Kwamishinan matasa da wasanni na Jihar Kano Alhaji Kabiru Ado Lakwaya ya ce nan bada dadewa ba za’a kammala gyaran filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata da kuma na Sabon Gari.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne ranar Laraba 10 ga watan Nuwamba, 2021 jim kadan bayan tashi daga wasan karshe na cin kofin Ahlan tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da Doma United.

Wasan karshen da aka gudanar a filin wasa na Ahmad Mu’azu dake sabuwar Jami’ar Bayero dake Kano.

Lakwaya ya kuma ce Kano Pillars ta zama abin kwatance a tsakanin kungiyoyin dake buga gasar Firimiya ta Najeriya.

Haka kuma Ado Lakwaya ya ce gwamnatin jihar Kano ta ware wasu kudade masu yawa domin siyawa kungiyoyin dake buga wasanni a jihar Kano kayan wasa domin kara musu gwarin gwiwa.

Ya kuma yabawa shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Kano Alhaji Sharu Rabiu Alhan bisa shirya gasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!