Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Victor Osimhen zai dawo daukar horo – Luciano Spaletti

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Napoli Luciano Spaletti ya ce dan wasan gaban Najeriya da Napoli Victor Osimhen zai dawo wasa a farkon watan da muka shiga Nuwambar 2021.

Osimhen ya ji rauni dai a wasan da kungiyar sa ta doke Salernitana a gasar cin kofin zakaru turai ta Europa.

Luciano Spaletti ya ce yana fatan dan wasan zai buga wasan da Napoli za ta buga da Verona a ranar lahadi 6 ga watan Nuwambar 2021, sai dai bazai samu damar buga wasan da za su buga a tasakiyar mako ba, a karawar da za su yi da Legia Warsaw a gasar Europa League.

Dan wasan mai shekara 22 ya buga wasanni 8 da kungiyar ta sa ta fafata, sai dai bai wakilce su a wasan da Napoli ta doke Salernitana ba.

Dan wasan ya buga mintuna 705 a kakar wasanni ta bana, inda ya jefa kwallaye biyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!