Labarai
Aikin Allah: Ganduje ya yi yafiya ga ɗauraru 90
Gwamnatin jihar Kano ta yiwa wasu ɗaurarru 90 afuwa, tare da ragewa wasu da dama shekarun da za su yi a gidan gyaran hali da tarbiyya.
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya ayyana yafiyar a ranar Litinin, yayin da ya ziyarci gidan gyaran hali da tarbiyya na Goron Dutse a wani ɓangare na bikin ƙaramar sallah.
“Mun tabbata kun saba ganin wannan hidima da muke yi a kowacce shekara sau biyu, muna yi da Sallah ƙarama da kuma babba”.
Ganduje ya ci gaba da cewa “Muna yin afuwa ne ga waɗanda muka tabbatar da halayyar su ta gyaru, wasu kuwa saboda tsufa wasu saboda rashin lafiya wasu kuwa ku don ya cancanci ace suna kabari a yanzu”.
Gwamna ya kuma ce “wannan ya sa wasu suke samun sassauci daga hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai, don haka muna fatan ku da kuka samu yafiya ku zama mutane na gari bayan kun fita zuwa iyalanku”.
Wakiliyar Freedom Radio Zahra’u Nasir ta rawaito cewa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kuma bukaci waɗanda suka rabauta da yafiyar da su je su yi rijistar koyon sana’o’in dogaro da kai waɗanda gwamnati ke samarwa.
You must be logged in to post a comment Login