Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wasu cikin muhimman al’amuran da gwamnatin jihar Kano ta gudanar a 2022

Published

on

  • A ranar 17 ga watan Yuni gwamna Ganduje ya kaddamar da gwajin aikin Hajji.
  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar wa majalisar dokokin kasafi a ranar 4 ga Nuwamba
  • A ranar 22 ga Disamba ne gwamnan ya ziyarci sabuwar kasuwar magani ta Dan Gwauro.

Ranar Asabar 28 ga watan Janairun shekarar 2022 ne gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya mika sandar mulki ga sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim, a fadarsa da ke Masarautar Gaya, biyo bayan rasuwar sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir.

A ranar 9 ga watan Fabarairun bara ne gwamna Ganduje ya karbi bakuncin mai dakin shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, tare da jagorantar tawagar ta ta zuwa gidan iyayen dalibar nan Hanifa, wadda malaminta ya hallaka bayan yin garkuwa da ita.

Inda suka mika sakon ta’azziyarsu cikin yanayi na alhini.

A ranar 5 ga wanta Mayun da ya gabata ne dai gwamna Abdullahi Ganduje ya ayyana mataimakinsa Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, inda Alhaji Murtala Sule Garo zai yi masa takarar maataimakin gwamnan.

Gwamnan ya ayyana sunayen na su a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnati.

A dai ranar 17 ga watan Yunin shekarar ne gwamna Ganduje ya kaddamar da gwajin aikin Hajji a aikace, a sansanin Alhazai da ke nan Kano.

Haka kuma a ranar 9 ga watan Yuli ne gwamna Ganduje ya yi wasu daurarru guda 90 afuwa, inda aka sake su daga gidan ajiya da gyaran hali na nan Kano.

Gwamna Ganduje ya karbi bakuncin jagororin kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar Kano a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata a fadar gwamnati, lokacin da suka gudanar da zanga-zangar lumana, don nuna goyon baya ga yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa ASUU.

Sai kuma ranar 2 ga watan Satumba gwamna ya rantsar da sabbin kwamishinoni guda goma sha daya, wadanda suka maye gurbin kwamishinonin da suka shiga neman takara.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci majalisar dokokin Kano a ranar 4 ga wantan Nuwamba domin gabatar da kasafin kudin bana, kuma kasafi na karshe a mulkinsa.

A ranar 22 ga Nuwamba ne gwamna Abdullahi Ganduje ya sanya hannu kan wasu dokoki guda goma sha daya, ciki har da dokar kafa hukumar kula da masu bukata ta musamman.

Sa hannun na zuwa ne jim kadan bayan da ya karbi bakuncin sabon kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano Mamman Dauda a gidan gwamnati.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kuma karbi rahoton aikin Hajjin da ya gabata a ranar 2 ga watan Disamba, har ma ya zargi hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON da gazawa.

Sannan kuma ya bude sabon masallacin juma’a dake sansanin Alhazai, don saukaka wa maniyyata gudanar da ibada kafin tafiya kasa mai tsarki da kuma bayan dawowarsu.

Haka zalika a ranar 22 ga Disamba ne gwamnan ya ziyarci sabuwar kasuwar magani da ake ginawa a garin Dan Gwauro.

Wani aiki na baya-bayan nan da gwamnatin jihar Kano gudanar shi ne na karasa aikin samar da wutar lantarki ta jihar Kano daga Dam din Tiga, har ma a ranar 24 ga wannan wata na Disamba gwamna Ganduje ya bayar da wa’adin makonni biyu ga kamfanin da ke aikin na lallai ya kammala shi, don samar da wutar da za ta haska fitulun titi, da kuma wuta ga matatar ruwa ta garin Tamburawa.

 

Rahoton: Abba Isah Muhammad

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!