Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin musulmi ya jajantawa al’ummar Hadejia kan ambaliyar ruwa

Published

on

Mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa a karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa da ambaliyar ruwa ta shafa.
Sarkin musulmin ya bayyana hakan ne a yau lokacin da ya halarci taron aza harsashin gina jami’a mai zaman kanta ta Assalam Global University wanda kungiyar Jama’atu Izalatil Bidia Wa Iqamatus Sunnah ta samar a karamar hukumar Hadejia.
Ya kara da cewa in aka yi la’akari da yadda ambaliyar taci zarafin gonaki da gidaje da wuraren ayyuka abin dubawa ne tare da taimakon wadanda abin ya shafa musamman a wannan lokacin da ake cikin matsi.
A nasa bangaren gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana farin cikinsa bisa ga wannan jami’a da kungiyar IZALA ta samar.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje na daga cikin wadanda suka halarci taron.
Inda a yayin taron aka tara kudade da dama da za a yi amfani dasu wajen aikin gina jami’ar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!