Labarai
Aikin Hajjin bana zai banbanta da na shekarun baya- NAHCON
Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta ce, tsarin aikin hajjin bana zai banbanta da sauran shekarun baya, ta hanyar samar da sabbin tsare-tsaren inganta rayuwar mahajjata a kasa mai tsarki.
Shugaban hukumar Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana hakan yayin kulla wata yarjejeniya da Kamfanin kula da mahajjatan da suka fito daga nahiyar Afrika wadanda ba larabawa ba, wanda aka gudanar a birnin Jeddah na kasar ta Saudiyya.
Hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON da Kamfanin kula da mahajjatan da suka fito daga nahiyar Afrika wadanda ba larabawa ba, sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar aiki da zasu gudanar a lokacin aikin hajjin wannan shekara ta 2023.
Yarjejeniyar ta samu sanya hannun shugaban hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON Alhaji Zikrullah Kunle Hassan da kuma shugaban Kamfanin kula da mahajjatan nahiyar Afrika wadanda ba larabawa ba Ahmad Sindy.
Wata sanarwa da hukumar ta NAHCON ta fitar mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan yaɗa labarai na hukumar Musa Ubandawaki, ta nuna cewa yarjejeniyar ta kunshi yanda Kamfanin zai kyautata tsarin hidima da ciyar da mahajjatan, tare da ragin kaso biyar cikin dari na kuɗaɗen da za’a biya na hidimar a wannan shekara.
Yayin tattaunawa ta musamman da ɓangarorin biyu suka gudanar a birnin Jeddah na kasar ta Saudia, sun mayar da hankali kan tsare tsaren da zasu gudana lokacin aikin hajjin, kama daga kan wayar da kan mahajjata, da koyar da su gami da zirga zirgarsu a tsawon lokacin gudanar da aikin hajjin na bana.
A jawabinsa tun da farko shugaban hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana rashin jin dadi game al’amarin da ya faru a shekarar da ta gabata kan wahalhalun da Alhazan Najeriya suka fuskanta daga ayyukan kamfanonin kula da mahajjatan, wanda yace ba ya fatan hakan ta sake faruwa, hakan ce kuma ta sanya su ƙulla wannan yarjejeniya domin sanin matsayar kamfanonin da kuma hidimar da zasu yi.
A lokacin da yake gabatar da tsare tsaren da suka shirya shugaban Kamfanin kula da mahajjatan a ƙasar Saudiya Ahmad Sindy, ya sha alwashin cewa matsalar da Alhazan Najeriya suka fuskanta a shekarar da ta gabata ba zata sake faruwa ba, sakamakon zage damtse da suka yi, wajen inganta ayyukan nasu a wannan shekara, domin saukakawa mahajjata da kuma samar musu da walwala da jin dadi.
Aikin hajjin wannan shekara ta 2023 ana sa ran zai fara ne daga ƙarshen watan Yuni.
You must be logged in to post a comment Login