Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Direbobin Tirela sun bude hanyar Kano zuwa Zaria

Published

on

Direbobin tirela da suka rufe babbar hanyar Kano zuwa Zaria, sun janye motocin su sakamakon halin da masu bin hanyar suka shiga bisa rufe hanyar.

Guda daga cikin wadanda suka rufe hanyar Ya’u Abdulhamid Usman, shi ne ya shaida hakan ga wakiliyar Freedom Radio Hafsat Abdullahi Danladi da safiyar yau Litinin ta wayar tarho.

Ya ce, direbobin sun bude hanyar ne saboda irin halin matsin da matafiya suka shiga bisa kulle hanyar wadda ke fama da kara-kainar al’umma daga sassa daban-daban na Najeriya.

A karshen makon da ya gabata ne muka kawo muku rahoto kan yadda direbobin tirelar suka rufe babbar hanyar Kaduna zuwa Kano sakamakon kashe dan uwan su da suke zargin wani jami’in soja ya yi, inda suka sha alwashin sai an biya su diyya sannan za su bude hanyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!