Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NAHCON za ta kaddamar da jirgin farko na maniyyata

Published

on

Hukumar kula da aikin Hajji NAHCON, ta ce, za ta kaddamar da jirgin farko na jigilar maniyya hajjin bana a ranar 25 ga watan Mayu da muke ciki, wanda zai fara diban maniyyatan jihar Nasarawa.

Shugaban hukumar ta NAHCON, Zikrullah Kunle Hassan, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da tawagar masu aikin yada labaran hajjin bana wanda aka gudanar a Abuja.

Zikrullah Kunle Hassan ya bukaci jami’an yada labaran da su sanya gaskiya da adalci a dukkanin rahotannin da za su bayar, kafin aikin hajjin da kuma lokacin yinsa har ma da bayan an kammala.

Ya kuma ce, tawagar ma’aikatan kula da aikin hajjin bana za su tafi kasa mai tsarki a ranar Lahadi mai zuwa don shirye-shiryen karbar maniyyatan Nijeriya, inda ya tabbatar da cewa aikin hajjin bana zai gudana ba tare da wata matsala ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!