Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Aikin jin kai: Gwamnati tarayya zata bai wa jihohi tallafin rage radadin ambaliyar ruwa

Published

on

Shugaban hukumar hasashen yanayi ta kasa Mr. Clement Nze ya ce, gwamnatin tarayya zata raba tallafi ga wasu jihohin kasar nan da ambaliyar ruwa ta shafa don rage musu radadi.

Clement Nze ya bayyana hakan ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a jiya Juma’a a birnin tarayya Abuja.

Ya ce, tuni gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti kan ambaliyar ruwa, da zai rika bibiyar ayyukan bada kayan rage radadin ga wadanda lamarin ya rutsa da su.

Nze ya kuma ce kwamitin zai yi gaggawar daukan matakan kare faruwar ambaliyar ruwa musamman wajen samar da dakuna a wasu jihohin don shirin ko-ta-kwana na samarwa wadanda ambaliyar ruwa ta ritsa da su muhallan zama na wucin gadi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!