Labarai
Akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu a rikicin Guma da Logo a jihar Benue
Wasu rahotanni na cewa akalla mutane 50 aka kashe a wani sabon rikici da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a kananan hukumomin Guma da Logo a Jihar Benue.
Rikicin wanda ya fara tun ranar daya ga wannan wata na sabuwar shekara, ya ci gaba da bazuwa har zuwa jiya Talata, wanda kuma ya zo a daidai lokacin da hukumomi a Jihar suka sanya dokar haramta kiwo barkatai.
Yankunan da tashin hankalin ya shafa sun hadar da Gambe-Tiev da Ayilamo da kuma Turan a karamar hukumar Logo, sai kuma Umenger da Tse-Akor da Tomatar da kuma Nongov a karamar hukumar Guma.
A zantawarsa da manema labarai bayan kamamla taron majalisar tsaron Jihar a Makurdi, gwamnan Jihar ta Benue Samuel Ortom ya zargi jami’an tsaro da gaza aikata katabus wajen kare al’umma daga fuskantar hare-haren, sai dai bai bada adadin mutanen da rikicin ya shafa ba.
Gwamna Ortom ya ziyarci wadanda suke asibiti suna karbar magani sakamakon jikkata da suka yi.
Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘yan-sandan Jihar Moses Yamu ya tabbatar da faruwar hare-haren da ya ce sun auku ne daga ranar Litinin zuwa jiya Talata, sannan kuma ya tabbatar da mutuwar mutane 17.