Connect with us

Labarai

Kamfanin NNPC ya ce kamfanin ya tace kaso 18.24 a cikin watan Oktoban bara

Published

on

Kamfanin mai na kasa NNPC ya ce matatu hudu da kasar nan ke da su sun tace litar mai dubu dari biyu da hudu da dubu talatin da daya ne kacal a cikin watan Oktoba na bara, wato kaso goma sha takwas da digo ashirin da hudu.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da manema labarai na kamfanin Ndu Ughamadu ya fitar jiya a Abuja.

 

Sanarwar ta ce a wannan wa’adi na watan Oktoba Kamfanin na NNPC ya shigo da litar mai miliyan dari tara da goma sha biyar da dubu arba’in da takwas daga ketare ko kuma kaso tamanin da daya da digo saba’in da shida.

 

Mr. Ndu Ughamadu ya kuma ce a watan na Oktoba ya raba litar mai biliyan daya da miliyan dari uku da hamsin da biyu da dubu tamanin da shida.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,340 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!