Connect with us

Kiwon Lafiya

Babbar kotun tarayya mai zamanta a Abuja ta bada belin Kanar Sambo Dasuki

Published

on

Babbar kotun tarayya mai zamanta a Abuja da bada belin tsohon mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki mai ritaya.

Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ce ta zartas da wannan hukunci a safiyar yau Litinin, inda ta bayyana tsare shin da aka yi da cewa ba daidai bane, ya saba da tsarin doka da oda.

Wannan dai shi ne karo na shida da ake bada belin Sambo Dasuki kuma a kan kudi Naira miliyan N200M,sai dai jami’an tsaron sirri na DSS sun ki bin umarnin kotun wajen sakinsa.

Kotun dai ba bada umarnin wadanda za su tsaya masa su kasance suna mataki na 16 a aikin gwamnati, idan kuma ba ma’aikata ba ne su kasance suna gidaje a Maitama da Asokoro ko Utaku ko kuma Garki.

Kuma za su ajiye kudi Naira miliyan dari a asusun Kotun.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,926 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!