Labarai
Akwai barazanar tsaro a ƙananan hukumomi 17 a kano – DSP Kiyawa
Tsaro:Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce akwai akwai barazanar tsaro a ƙananan hukumomin Kano 17.
Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya bayyanawa Freedom radio hakan.
Ya ce, shigowar bakin fuska jihar Kano ya sanya aka gano ƙanan hukumomin da za su iya fuskantar matsalar tsaro.
A don haka ya buƙaci al’ummar da suke kan iyakokin jihohin Kano da su kula da mutanen da ke shigowa.
“Da zarar an ga baƙon fuska wanda ba’a yadda da shi ba, ai gaggawar bayyanawa jami’an tsaro ko masu rike da masarautun gargajiya don magancewa”.
Kiyawa ya kuma ce kasancewar an hana sayar da man bunburutu a wasu jihojin, wasu na shigowa suna saya suna kai wa jihohin, a don haka ya ce al’umma su ƙara sanya idanu a kan wannan lamarin .
Akwai barazar tsaro a kanann hukumomi 17 a kano-rundunar yan sandan kano
You must be logged in to post a comment Login