Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Akwai barazanar tsaro a ƙananan hukumomi 17 a kano – DSP Kiyawa

Published

on

Tsaro:Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce akwai akwai barazanar tsaro a ƙananan hukumomin Kano 17.

Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya bayyanawa Freedom radio hakan.

Ya ce, shigowar bakin fuska jihar Kano ya sanya aka gano ƙanan hukumomin da za su iya fuskantar matsalar tsaro.

A don haka ya buƙaci al’ummar da suke kan iyakokin jihohin Kano da su kula da mutanen da ke shigowa.

“Da zarar an ga baƙon fuska wanda ba’a yadda da shi ba, ai gaggawar bayyanawa jami’an tsaro ko masu rike da masarautun gargajiya don magancewa”.

Kiyawa ya kuma ce kasancewar an hana sayar da man bunburutu a wasu  jihojin, wasu na shigowa suna saya suna kai wa jihohin, a don haka ya ce al’umma su ƙara sanya idanu a kan wannan lamarin .

Akwai barazar tsaro a kanann hukumomi 17 a kano-rundunar yan sandan kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!