Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Akwai bukatar mutane su san kundin dokar shari’a ta 2019 – Kungiyar KCSF

Published

on

Hadakar kungiyoyin sa kai na farar hula masu zaman kansu a jihar Kano wato Kano Civil Society Forum (KCSF), tare da hadin gwaiwar tarayyar turai EU, da kungiyar yada al’adun kasar Birtaniya ta British Council , da kungiyar tabbatar da doka da yaki da cin hanci ta Rule of Law and Anti-corruption (Rolac), sun gabatar da makalar wayar da kai dangane da kundin tafiyar da shari’ar laifi ta shekara 2019.

Taron wanda ya gudana a cibiyar Dimokradiyya da fadada bincike ta Aminu Kano dake gidan Mumbayya, ya yi duba akan sabbin dokoki da yadda tsarin gudanar dasu yake ga al’umma wanda aka shiryawa kungiyoyin farar hula dake Kano 150 da ‘yan Jarida.

Da yaje jawabi Babban mai gabatar da makalar, Dakta Nuhu Musa Idris , na sashen koyar da shari’a ta Jami’ar Bayero dake nan Kano, ya yi tsokaci kan wasu dokokin da suka fi sarkakiya inda yayi kira da a duba wasu dokokin da suka tsufa sakamakon shari’a na tafiya da Zamani.

A bagaren sa, shugaban hadakar kungiyoyin fararen hula na jihar Kano (KCSF) Ibrahim Wayya, ya ce rashin sanin dokokin ya taka rawa matuka wajen take hakkin al’umma da yasa ake da bukatar sanin yadda suke.

Wasu mahalarta taron wanda shi ne irin sa karo na uku da aka shirya , a shiyyoyin Sanatoci Kano guda uku, daga kungiyoyin farar hula sun bayyana yadda suka kalli tsarin dokokin da sakon su.

Wakilin mu Aminu Halilu Tudunwada, da ya halarci taron wayar da kan , ya ruwito mana cewa an tattauna matsalolin wasu dokoki da aka tsakuro da al’umma ke fuskantar Kalubale a kan su wanda galibi basu san hakkin su ba akan su , kasancear dokar tana da dokoki sama da 400, da suka yi Karin bayanan wayar da kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!