Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

 Kotu ta dage sauraran karar Abba Kabir kan zargin Ganduje da saida kadarorin gwamnati

Published

on

Babbar kotu a jihar Kano ta dage ci gaba da saurarar karar da dan takarar gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shigar ya na kalubalantar gwamnan Kano Abdullaji Umar Ganduje kan sayar da wasu daga cikin kadarorin gwamnati.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isam’il ya ruwaito cewa ,a  yayin zaman kotun na yau, mai shari’a Nura Sagir ya dage saurar karar, har zuwa ranar 29 ga watan Oktobar shekarar da muke ciki.

Lauyan Abba Kabir Yusuf, wato Bashir Yusuf Tudun Wuzirici ya  ce matakin da gwamnan jihar Kano ya dauka na saida kadarorin gwamnatin ya sabawa  dokar tasarafi da filaye ta jihar Kano.

Ya yin da lauyan gwamnatin Kwmishinan shari’ar Barrista Musa Abdullahi Lawal ya ce korafin bashi da tushe ballantana makama.

Muna dauke da cikakken labarin a nan gaba

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!