Labarai
Akwai bukatar mutane su kara kaimi kare kansu daga cutar Maleriya- WHO
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci al’umma da su rinka kare kansu daga kamuwa cutar zazzabin cizon sauro wanda ke kisa farat daya, musamman ga mata masu juna-biyu da kuma kananan yara.
A cewar WHO a cikin shekaru biyun da suka gabata, ta ceto masu fama da cutar zazzabin cizon sauro sama da billiyan biyu, sannan ta kare masu juna-biyu da kananan yara sama da miliyan goma sha daya a fadin duniya.
Hakan manuniya ce da cewa yana da kyau mutanen da suke wannan yanki dasu kara kaimi wajen ganin sun fatattaki wannan matsalar.
Freedom Radio ta tuntubi Farfesa Isa Abubakar darakta a ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano, kan abubuwan da suke haifar da cutar zazzabin cizon sauron da kuma alamominta, wanda ‘ya tabbatar da cewa macen sauro ce take haifar da cutar zazzain cizon sauron, wacce idan ta zuki jinin mai dauke da cutar, ta kuma sakawa wani, sai ya kamu da cutar.
A cewarsa ‘cutar tafi Kamari ne ga kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar, sakamakon raunin garkuwar jikin da suke da ita, inda su kuma mata masu juna biyu take musu ila biyo bayan rashin kwana a gidan sauro mai dauke da magani’.
Tare da cewa ‘daga cikin abubuwan da suke haddasa cutar akwai rashin cikakkiyar tsabta da kuma rashin gyara magudanar ruwa da dai sauransu’.
Farfesa Isa ya kuma ce’alamomin cutar zazzabin cizon Sauron sun hadar da rawar dari da ciwon kai ko ciwon gabobi ko kuma fitsari ya koma aki kirin, yayin da wasu ta ke kaisu ga suma ma.
‘Matakan kariya daga kamuwa da cutar kuwa sune kiyayewa daga abubuwan da suke haddasa kamuwa da cutar’, a cewa Farfesa Isa Abubakar.
You must be logged in to post a comment Login