Labarai
Akwai hatsari cikin yaɗa labaran ƙarya musamman a watan Azumi – Dr. Ruƙayya
Yayin da aka shiga wata mai alfarma na Ramadan masana a fagen yada labarai sun gargadi al’umma kan su kaucewa yaɗa labaran ƙarya na bogi game da ibada ko kiwon lafiya.
Da take zantawa da Freedom Radio, Dr. Ruƙayya Yusuf Aliyu ta sashen koyon aikin jarida na jami’ar Bayero ta ce, akwai buƙatar al’umma su ƙara lura sosai da irin saƙonnin da wasu ke amfani da su a wannan lokaci wajen aikewa mutane, tare da neman su ƙara yaɗa shi.
Dr. Ruƙayya ta ce, akwai bukatar jama’a su riƙa taka tsan-tsan game da irin saƙonnin da ba su da tabbacin ingancinsu domin gudun fadawa tarkon labaran ƙire.
Ta ce, abin takaici ne yadda ake ƙara samun yawaitar labaran ƙanzon kurege a tsakanin al’umma, musamman a ce abu ya kai ga yin amfani da addini.
Ta kuma yi kira ga malamai da shugabanni da kafafen yaɗa labarai, kan su yi amfani da damar su wajen ƙara wayar da kan al’umma kan illar da hakan kan haifar.
You must be logged in to post a comment Login