Labarai
Akwai rashin kyawun hanya a Kano – Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya koka kan rashin kyawun hanyoyin sufuri a Kano.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana hakan ne a wajen taron wata muƙala da aka shirya a garin Bichi a wani ɓangare na bikin ba da sanda.
Ƙorafin na sa ya biyo bayan yadda ya taso daga jihar Sokoto zuwa Kano, sai dai kafin Ƙarasawarsa garin Bichi ya dauki tsawon lokaci a hanyar.
“Na sha wahala matuƙa kafin na ƙaraso wajan wannan taro, domin kuwa na shafe sama da awa guda a hanya, sakamakon rashin kyawun hanya a Fanisau dalilin jar ƙasa da kwazazzabai, da kuma cunkoson ababen hawa a Kurna”.
Sarkin Musulmi ya ce, “Lokacin da na zo Kurna na ga tarin cunkoson ababen hawa a hanyar, wanda hakan ya sa dole na sauaya hanya na shiga ta cikin garin Fanisau, tafiyar da na yi daga jihar Sokoto zuwa Jihar Kano, ita na yi daga cikin garin Kano zuwa Bichi”.
Alhaji Sa’ad Abubakar, ya buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta mayar da hankali wajen magance matsalar cikin hanzari.
You must be logged in to post a comment Login