Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci CBN ya kara wa’adin daina karbar tsohon kudi

Published

on

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bukaci babban bankin Najeriya CBN, da ya kara wa’adin da ya sanya na daina amfani da tsofaffin kudaden daga ranar 31 ga watan nan da muke ciki na Janairu.

Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya baiyana hakan ne yayin da ya karbi bakunci Kwanturolan CBN na jihar Sokoto Dahiru Usman da jami’an babban bankin ranar Alhamis din makon nan a fadarsa.

Haka kuma ya kara da cewa, ya lura da yadda mutane da daama ba su da masaniya kan sabbin kudaden da aka sauya musamman ma wadanda ke rayuwa a yankunan karkara.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kuma bayyana matsalar rashin tsaro a matsayin babban kalubale la’akari da cewa, al’umma da dama ba za su iya dauko makudan kudaden su daga kauyuka zuwa bankuna ba, sakamakon fargabar ‘yan fashi da ‘yan bindiga.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!