Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Gwamnatin Jihar Kano zata hana mata bara

Published

on

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin jihar Kano tace zata fito da wasu tsare tsare da zata hana mata barace barace a titunan jihar Kano.

Daraktar kula da harkokin mata a ma’aikatar mata ta jihar Kano Hajiya Kubra Dankani ce ta bayyana hakan lokacin da take tattaunawa da filin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio .

Hajiya Kubra tace barace baracen da mata ke yi a wasu titunan jihar Kano abu ne na damuwa wanda ya hada da sakacin mazajen su.

Tace duk da wannan halaye da mata suka shiga a jihar Kano ma’aikatar kula da walwalar matar ta jihar Kano na fito da tsare tsare da suke taimakawa mata a fadin jihar Kano.

Ministar harkokin mata Aisha Jummai Alhassan ta yi murabus daga mukamin ta

Matasa sun yi zanga-zanga kan aikin Titin Five Kilometer

Tace maaikatar mata ta hanyar ofishinta na bawa mata marasa karfi tallafi na sana’oi da suke aiwatarwa da sauran su.

Hajiya Kubra ta kara da cewa bayan tallafi da suke bawa mata ,tace matan da suka rasa mazajansu ko ta hanyar guduwa maaikatar na biya  musu kudaden haya idan akayi bincike kuma aka tabbatar gaskiya  ne.

Hajiya Kubra Dankani tace gwamnatin jihar Kano ta damu matuka a game da barace baracen da mata ke yi akan titunan jihar Kano musamman ma da daddare.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!