Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Karatun mata zai kawo cigaban al’umma

Published

on

Daga Umar Idris Shuaibu

Shugaban kungiyar nan mai zaman kanta ta mata da matasa don samar da zaman lafiya da adalci,  wato ‘Women and Youth for Justice and Peace’ dake nan Kano Dr. Jummai Alhamdu ta ja hankalin mata da su rubanya kokarin su wajen gudanar da rayuwa mai kyau,  a wani mataki na samar da al’umma ingantacciyya.

Dr. Jummai Alhamdu ta bayyana hakan ne yayin taron da cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma CITAD ta shiryawa dalibai mata da aka gudanar a dakin taro na hukumar kula da makarantun sakadaren ta jihar Kano.

Mahalatta taron

Dr. Jummai Alhamdu ta ce shakka babu,  akwai bukatar mata da matasa dake makarantun sakandare su maida hankali wajen rungumar ta’adu na kwarai,  kasancewar gudunmawar da suke bayarwa wajen gina al’umma na da yawan gaske.

Ta ce abin alfahari ne mata matasa su zage dantse a bangarorin karatun su,  don kuwa sune za su zama makarantar farko ga ‘ya’yan su.

Ta kara da cewa,  ‘galibi shekarun yarinta shine lokacin da za su tsaya su   koyi abubuwan da za su kawowa jama’a ci gaba,  da suka shafi bangaren zamantakewar rayuwar su da ilmi’.

Da yake jawabi, mukaddashin babban daraktan cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma ta CITAD, Malam Ahmad Abdullahi Yakasai,  ya ce manufar su ta shirya irin wannan zama shine don nusar da matasa fuskantar kalubalen rayuwar su, idan suka ji fadi-tashin da manyan mutane suka yi a bangarori daban-dabam na rayuwa.

Ilimin ‘ya’ya mata zai gyara rayuwar al’umma –Yariman Kano

Dokar kafa hukumar bunkasa ilimi na jihar Kano ya tsallake karatu na 2

Shi kuwa shugaban hukumar kula da makarantun sakandare ta jihar Kano,  Dr. Bello Shehu ya ja hankalin daliban da suka samu halartar taron,  da suyi dukkan mai yiwuwa wajen ganin sun kere sa’a a sha’anin karatun su.

Dr. Bello Shehu ya kara da cewa, gwamnatin jihar Kano tayi tsare-tsare don ciyar da ilmin makarantun sakandare garambawul a matsayin shi na daya daga cikin ginshikan gina al’umma mai ilmi.

Bisa al’ada daiCITAD din na shirya taron da ake yiwa take da ‘ILERIS’ duk wata a cibiyar ta su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!