Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Akwai yiwuwar ci gaba da fuskantar wahalar Fetur a wasu jihohin Nijeriya

Published

on

Har kawo yanzu haka dai rahotanni na nuni da cewa akwai yiyuwar ci gaba da fuskantar rashin wadatuwar Man Fetur a birnin tarayya Abuja har ma da wasu jihohin Arewacin kasa.

Haka kuma rahotoonin sun nuna alamun cewa wahalar Fetur din wadda yan Nijeriya ke fama da ita tun watannin baya, za ta ci gaba da faruwa har zuwa bayan kammala zaben gwamnoni da za’ayi a ranar Asabar mai zuwa.

Karancin Fetir din dai ya fi ta’azzara a Abuja da Neja da kuma wasu jihohin yankin Arewa, inda kadan daga ciki gidajen Mai ne kadai ke siyar da shi a farashi mabambanta.

Farashin kowace lita guda dai ya kai naira dari hudu a gidajen man da ke dillancin sa, yayin da na ‘yan bunburutu a ke sayar da lita naira dari hudu da hamsin zuwa dari biyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!