Kiwon Lafiya
Akwai yiwuwar samun karancin abinci a jihohi 16 na Arewacin Najeriya-FAO
Hukumar kula da Samar da abinci dan inganta ayyukan gona ta duniya FAO ta yi gargadin cewar akwai yiwuwar samun matsananciyar matsalar karancin abinci da za ta shafi kusan mutane miliya 4 a jihohi 16 da ke Arewacin Najeriya
A cewar hukumar ta FAO, da kuma hukumar bayar da agajin abinci ta Majalisar dinkin duniya WFP, matsalar za ta shafi hatta birnin Tarayyar Abuja, muddin aka gaza daukar matakan gaggawa.
FAO da kuma WFP sun ce jihohin da matsalar za ta shafa sun hada da Bauchi, Benue, Gombe, Jigawa, Plateau, Niger, Kebbi, Katsina, Kaduna, Taraba, Zamfara, Sokoto, Kano, Yobe, Borno da kuma Adamawa.
A don haka ne hukumomin biyu suka shawartar hukumomin a kasar nan da kuma jihohin da al’amarin zai sahafa da su dauki matakin gaggawa domin kaucewa fadawa cikin matsalar ta yunwa.