Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Al Sadd ta amince Xavi Hernandes da ya koma horar da tsohuwar kungiyar sa ta Barcelona

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Al Sadd dake kasar Qatar, ta ce Barcelona ta biyata dukkanin kudaden da suka kamata, domin daukan mai horar da ‘yan wasan ta kuma tsohon dan wasan na Barcelona Xavi Hernandes a matsayin mai horarwarta.

Hakan na cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar a shafinta na Twitter a yau Juma’a 5 ga watan Nuwambar 2021.

Sanarwar ta ce tuni kungiyar ta Al Sadd ta amince da bukatar Barcelona na daukar mai horar da ‘yan wasan na ta Xavi Hernandes.

Kazalika sanarwar ta ce Xavi tun a kwanakin baya ya sanarwa da kungiyar ta Al Sadd kudurin sa na san zuwa Barcelona duba da  mawuyacin halin da take ciki a halin yanzu wanda hakan yasa ta amince da kudurin nasa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!