Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Alfanun dake tattare da gwaji kafin aure

Published

on

Wani kwararren likita a sashen kula da lafiyar al’umma dake asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano Dakta Abdullahi Isa Kauran Mata ya ja hankalin al’umma musamman masu niyyar yin aure da su himmatu wajen yin gwajin lafiyar su kafin aure.

Dakta Kauran mata ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da wakilin Freedom Radio Umar Idris Shuaibu.

Ya ce ya zama wajibi a baiwa tsarin yin gwajin kafin aure muhimmanci domin zama babban mataki na kare yaduwar cutuka tsakanin al’umma.

Likitan ya kara da cewa, kasancewar addinin musulunci ya bayar da damar aurar mace ta fiye da daya, alama ce dake nuna cewa idan al’umma basu kula ba, shakka babu zai zama hanya ta yada cutuka idan ba a baiwa gwaji kafin aure muhimmanci ba.

Yin gwajin lafiyar ga masu niyyar yin aure na zaman bunkasa matakin lafiyar al’umma, da kuma wayar dan mutane kan mutane da ya kamata suyi aure idan kwayoyin halitta sun yi dai-dai.

Dakta Abdullahi Kauran Mata ya ce galibi mutane kan yi shakulatin bangaro da wannan dama da suke da ita na yin gwaji akan lokaci kafin aure.

Mahukunta a Birnin Dutse dake jihar Jigawa sun sanya gwaji kafin aure ya zama doka ga duk wanda zai yi aure a yankin, a wani mataki na kare lafiyar mutane daga yada cutar amosanin jini ga ‘ya’yan su.

Dakta Abdullahi Kauran Mata ya kara da cewa, ya zama wajibi ga masu shirin yin aure su je cibiyoyin gwajin lafiya don auna su, duba da muhimmancin hakan ga lafiyar su.

An sake samun wata mata da ake zargi da auren maza biyu a Kano

Nazari kan halin da yaran da aka haifa bata hanyar aure ba

Laifin iyaye ne ke haifar da mace-macen aure -Hisbah

Likitan ya kuma shawarci iyaye da kuma masu shirin yin aure su fahimci alfanun dake tattare da da yin gwaji akan lokaci kafin kusantowar aure, wanda idan ba a dauki irin wannan mataki ba, hakan yana bayuwa ga shakuwar da za ta janyo rashin iya rabuwa ko dai wata matsala ta daban ga masu niyyar yin auren.

Shi kuwa limamin masallacin Juma’a na Usman Bin Affan dake Gadon Kaya a cikin Birnin Kano, Malam Abdallah Umar Usman Gadon Kaya, ya ce addinin musulunci ya kwadaitar da mutane wajen kiyaye lafiyarsu don samar da al’umma nagartacciyya.

Kwararru a bangaren kiwon lafiya sun bayyana cewa, idan al’umma suka yi kyakkyawan amfani da wannan dama ta gwaji kafin aure, shakka babu zata taimaka wajen dakile yaduwar cutuka kamar mai karya garkuwar jiki da cutar hanta da dai sauran su a tsakanin al’umma.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!