Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Majalisar dokokin jiha zata magance matsalolin muhalli

Published

on

Majalisar dokoki ta  bayyana cewa za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an magance matsalolin muhalli a fadin jihar Kano.

Shugaban kwamitin kula da harkokin muhalli na majalisar,  wakilin karamar hukumar Takai a majalisar Alhaji  Musa Ali Kachako,  ya bayyana haka a ziyara zuwa ofishin hukumar aikin dakile zaizayar kasa da ambaliyar Ruwa ta kasa shiyyar Kano.

Musa Ali Kachako,  kara da cewa lamarin muhalli abu ne da ya kamata a dube shi da muhimanci tare  da bullo da  hanyoyin da za a magance matsalar sa.

Karin labarai:

Shin ina makomar matsalar gurbatar muhalli a Jihar Kano

Majalisar zartaswa ta amince da fitar da Naira Miliyan 977don samar wa hukumar fasa kwauri muhalli

A ya yin ziyarar   Alh Musa Shuaibu , ya ce  gwamnatin tarayya ce ta bayar da aikin tun a shekara ta 2012 da nufin magance matsalar kwararowar Hamada da matsalar zaizayar kasa a fadin kasar nan.

In da yace an   kaddamar da aikin ne a nan Kano a shekarar 2017, wanda an samu cigaba kwarai  na  dashen bishiyu da gina madatsar ruwa da sauran wasu manyan ayyuka, musamman  guraren dake fuskantar barazanar Hamada.

Wakilinmu Auwal Hassan Fagge, ya  ce  Alhaji  Musa Shuaibu, ya bukaci da a sakarwa takwarar  hukumar  ta jihar Kano kudade cikin gaggawa   don cigaba da ayyukanta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!