Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Laifin iyaye ne ke haifar da mace-macen aure -Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta alakanta matsalar mace-macen Aure a yanzu da rashin sauke hakkin da Allah ya dorawa mazajen ta bangaren kula da yalansu.

Babbar kwamandan hukumar ta Hisba bangaraen mata Malama Ummulkulsum Kasim ce ta bayyana hakan, bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar freedom radiyo da ya mayar da hankali kan yadda za’a magance matsalolin aure cikin wannan al’umma.

Malama Ummulkulsum ta kara da cewa, mafi yawan gurbacewar tarbiyyar ya samo asali ne daga rashin kyakkyawar alakar Aure tsakanin iyaye wanda hakan ke sanya yaran su rasa kulawar da ta dace daga iyayensu.

Hisbah ta cafke matashi kan yunkurin haikewa budurwar abokinsa

Hisbah ta cafke masu Kanjamau

Hukumar Hisbah ta kama mabarata anan Kano

 

A nata bangaran wata matashiya da ta kasance cikin shirin kuma take wakiltar ‘ya ‘ya mata Hauwa Shuaibu Gaya, ta alakanta matsalar da ake samu a zamantakewar  Aure da cewa rashin tarbiyya ne da ake samu tun daga gida kafin ma ayi Aure.

Bakin biyu sun yi kira ga iyaye maza da mata da su rika kula da yadda zasu tsara zamantakewar auren su domin tabbatar da samar da tarbiyya ta gari ga zuriar su.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!