Labarai
Alhazai 2006 akayi jigila zuwa kasa mai tsarki- NAHCON

Hukumar alhazai ta kasa ta ce ya zuwa safiyar yau asabar ta yi jigilar maniyyata 2,006 zuwa ƙasa mai tsarki.
Hukumar ta bayyana hakane a shafinta na X cewa jirgin MaxAir ya tashi daga birnin Bauchi zuwa Madina, inda ya kwashi maniyyata 384 da kuma jami’i guda ɗaya.
Wannan dai shi ne jirgi na biyar da suka yi jigilar maniyyatan daga ranar da aka ƙaddamar da jigilar wato ranar Juma’a zuwa yau.
You must be logged in to post a comment Login