Labarai
Ali Ndume ya dora alhakin sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kallon suna da matsala da mulkin Tinubu

Tsohon bulaliyar Majalisar Dattawa kuma Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya dora alhakin sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kallon suna da matsala ta musamman wajen kare hakkin dan Adam a kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma Majalisar Dattawa.
Sanata Ndume ya bayyana cewa wannan matsayi da Shugaban Amurka Donald Trump ya bai wa Najeriya, ya samo asali ne daga abin da ya kira gazawar gwamnati da majalisa, wajen kare hakkin dan Adam, da tabbatar da adalci da kuma kyautata tsarin mulki.
Ya ce irin waɗannan kura-kurai na iya rage martabar kasar nan a idon duniya, tare da haifar da ƙarin matsin lamba daga ƙasashen ƙetare kan yadda ake tafiyar da mulki a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login