Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Aliyu Bakinzuwo ya nemi afuwar Afakallah kan kalaman ɓatanci

Published

on

Wani matashi Aliyu Sabo Bakinzuwo ya nemi afuwar shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano kan kalaman ɓatancin da yayi masa.

A wata ganawa da manema labarai, Bakinzuwo ya nemi afuwar Isma’ila Na’abba Afakallah game da wasu kausasan kalamai da yayi masa ta wani zauren WhatsApp.

A cikin kalaman dai Aliyun ya yiwa Afakallah zagin tsamar nama kan ayyukan hukumarsa.

Sai dai a yanzu ya ce, yayi nadama saboda haka yake neman afuwar Afakallahun kan ya yafe masa.

A nasa ɓangaren shugaban hukumar tace fina-finai Isma’il Na’abba Afakallah ya ce, yafe cin zarafin da matashin ya yi masa.

Na’abba ya ja hankalin matasa masu amfani da kafafen sada zumunta kan su guji cin zarafin jama’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!