Labarai
Alkali na dogaro da hujja ne wajen yanke hukunci – Baba Jibo
Kakakin babbar kotun jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya musanta zargin da ake yiwa alkalai na yin rashin adalci a yayin yanke hukunci.
Baba Jibo Ibrahim ya musanta wannan zargi ne ta cikin shirin ‘yanci da rayuwa da ya mayar da hankali kan zargin alkalai da yanke hukunci bisa son rai.
Baba Jibo ya ce Alkali yana aiki ne dai ya shaidar da aka gabatar a gaban sa kuma da ita kadai zai dogara wajen yanke hukunci, a don haka duk wanda ya ji an yi masa rashin adalci to shine bai gabatar da kwararan hujojji ba.
Shi kuwa kakakin kula da gidajen gyaran hali na jihar Kano Musbahu Lawal Kofar Na’isa a cikin shirin cewa ya yi rashin cikakkakiyar doka ita ke ta’azzara rashin adalci a yayin shari’a.
Musbahu ya kuma ce “rashin kyakyawan binciken kafin yanke hukunci na kara yawan cunkoso a gidajen gyaran hali.
Shi kuwa wani bawan Allah da aka zanta da shi a cikin shirin, ya ce ya shafe tsahon shekaru 6 a gidan gyaran hali kan laifin da bai aikata ba.
Ya ce “an zarge shi da yiwa ‘yar sa ciki amma ba’a gudanar da wani kwakwaran bincike ba aka aike da shi gidan gyaran hali”
Yace daga baya an gano cewa ba shi da laifi kuma kotu ta bada umarnin biyan sa diyyar naira miliyan daya amma har yanzu ba’a biya shi ba.
You must be logged in to post a comment Login