Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Allah ya yi wa ɗan majalisar dokokin Kano na Ɓagwai/Shanono

Published

on

Allah ya yi wa ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar ƙananan hukumomin Ɓagwai da Shanono rasuwa.

Da safiyar yau Lahadi ne aka gudanar da jana’izar ɗan majalisar Alhaji Halilu Ibrahim Kundila, wanda Allah ya yi masa rasuwa a daren jiya Asabar.

An dai yi jana’izar marigayin ne a garinsu na Kundila da ke karamar hukumar Shanono.

Marigayi Alhaji Halilu Ibrahim Kundila, wanda aka zabe shi a matsayin dan majalisar jiha a jam’iyyar APC a zaben da ya gabata na bara, ya rasu ya na da shekaru 59 a duniya, kuma ya bar mata 4 da ‘ya’ya 17.

Kafin rasuwarsa, ɗan majalisar shi ne shugaban kwamitin karɓar ƙorafi na majalisar dokokin jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!