Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Ana zargin matashi da kashe kannensa 2

Published

on

Ana zargin wani matashi da kashe kannensa mata guda biyu a unguwar Hausawa da ke Mandawari a yankin karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa matashin mai suna Najibullahi ana zargin ya hallaka kannen nasa ne ta hanyar dukan su da muciya har sai da suka rasu sakamakon barinsa a gida tare da yaran bayan iyayensu sun fita.

Alhaji Lawan Bala Umar shi ne mai unguwar Hausawa ya tabbatar da faruwar lamarin ya na mai cewa, ” Gaskiya ne wannan mummunan al’amari ya faru, amma ni ban san yaron da ya aikata hakan ba, sai dai na ji an ce ya na da tabin hankali.”

” Ina kira ga iyaye da su daina barin ‘yayansu su kadai a gida, idan kuma za su yi hakan to su san da wa za su rika hada su don gudun irin wannan matsala,” inji Mai unguwa.

Tuni dai jami’an tsaro suka dauke gawarwakin yaran tare da kai su asibiti a wani mataki na fara gudanar da bincike kan lamarin.

 

Rahoton: Madina Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!