Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Allah ya yi wa Alhaji Musa Gwadabe Rasuwa

Published

on

Allah ya yi wa daya daga cikin jiga-jigan dattijan siyasar jihar Kano Alhaji Musa Gwadabe Rasuwa.

Rahotonni sun bayyana cewa, marigayin ya rasu ne a cikin daren jiya Talata a Kano bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 91 a duniya, inda ya bar mata da ƴaƴa da jikoki da dama

Alhaji Musa Gwadabe ya kasance a matsayin Minista lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa  2003, kuma Sakataren gwamnatin jihar Kano zamanin mulkin Sabo Bakin Zuwo.

Haka kuma har zuwa rasuwarsa, ya kasance mamba a jam’iyyar APC kuma shugaban shugaban gudanarwar hukumar ITF.

Za ai jana’izarsa da karfe 2:00 na rana, a gidansa da ke Maiduguri road a jihar Kano.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!