Labarai
Allah ya yi wa Sarkin Gusau Dakta Ibrahim Bello rasuwa

Sarkin Gusau a jihar Zamfara, Dakta Ibrahim Bello, ya rasu a safiyar yau Juma’a yana da shekara 71, bayan fama da doguwar jinya a Abuja.
Marigayin shi ne sarki na 16 a jerin sarakunan Gusau, kuma ya gaji mahaifinsa da ya rasu a ranar 16 ga watan Marisdin shekarar, 2015.
Gwamnan jihar ta Zamfara Dauda Lawal ya tabbatar da rasuwar sarkin a cikin wata sanarwar da mai magana da yawunsa Suleiman Idris ya fitar tare da bayyana jimamin gwamnatin jihar bisa babban rashin.
Marigayin ya shafe shekaru 10 da wasu watanni yana kan karagar mulki inda za a yi wa sarkin jana’iza a yau Juma’a a garin Gusa dake jihar.
You must be logged in to post a comment Login