Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Gusau ya zargi wasu ‘yan Zamfara da taimakawa ‘yan bindiga

Published

on

Sarkin Gusau a jihar Zamfara Alhaji Ibrahim Bello ya ce wasu daga cikin ‘yan jihar suna taimakawa ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane waje sayar musu da gidaje ko basu haya.

Sarkin na Gusau ya bayyana hakan ne lokacin da babban Sepeton ‘yan sanda   na  kasa, Muhammad Adamu Abubakar ya kai masa ziyara.

Alhaji Ibrahim Bello ya ce sun zauna da masu ruwa da tsaki a jihar domin kawo karshin matsalar da ake fusakanta ta ta’addaci a jihar sai dai abin  yaci tura.

A cewar sa bayar da haya ga  wasu al’umma jihar keyi, na taka rawa wajen yadda bata garin suke yin sojan gona suna shiga cikin jama’a suna aikata miyagun laifuka.

Alhaji Ibrahim Bello ya ce yan ta’addar na amfani da wannan damar ta zama a cikin al’umma suna kuma cin zarfin wadanda basuji ba basu gani ba,

Da yake jawabi a yayin ziyarar, babban Sefeton yan sandan kasar nan, Mohammad Adamu ya ce za suyi kokari wajen hada hannu da sauran jami’an tsaron kasar nan ganin an karkarde ayyukan bata gari a fadin kasar baki daya.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!