Labarai
Al’umma na cikin mawuyacin hali – Inji masu bukata ta musamman
Gamayyar kungiyoyin masu bukata ta musamman ta kasa, sun nuna rashin jin dadin su na yanayin da kasar nan take ciki musamman ma na tsadar rayuwa da halin ko in kula da matsantawa ga masu bukata ta musamman da ake yi ba tare da samar musu da mafita ba.
Shugaban gamayyar kungiyoyin magoya bayan jam’iyyar APC ta kasa na masu bukata ta musamman Yarima Sulaiman Ibrahim ne ya bayyana hakan a wani taro da suka gudanar don bayyana kalubalen da suke fuskanta.
Yarima Sulaiman, ya kara da cewa bai kamata ace gwamnatin da suka kyautatawa zato za ta yi halin ko in kula dasu ba, musamman yadda ake kama masu bukata ta musamman a jihohi da dama na kasar nan, ciki har da rusa musu muhallan su da gwamnatin jihar Kaduna ta yi a baya bayan nan.
Shima a nasa jawabin, sakataren kungiyar Ahmad Idris ya ce, a yanzu da dama daga cikin masu bukata ta musamman sun kama sana’o’in dogaro da kai don kaucewa yawon bara amma duk da hakan bai hana su fuskantar tsangwama da kame su ba musamman ma a birnin tarayya Abuja.
Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi, ya ruwaito cewa, gamayyar kungiyar suna fatan gwamnati ta waiwaye su tare da duba bukatun su, wanda kin yin hakan zai tilasta su fitowar su zanga-zanga da yin addu’a ta Alkunutu ga dukkan gwamnatoci a kowanne matakai.
You must be logged in to post a comment Login