Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

RIFAN za ta tallafawa manoman da ambaliyar ruwa ta shafa a Kano

Published

on

Kungiyar manoman shinkafa ta kasa reshen jihar Kano (RIFAN), ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa don ganin manoman da suka yi asara sakamakon Ambaliyar Ruwa a daminar bana sun samu tallafin da zai rage musu radadin asarar da suka yi.
Shugaban kwamitin dake lura da Iftila’i na kungiyar Hassan Muhammad Shuaibu ne ya bayyana hakan a tattaunawar sa da Freedom Radio, dangane da iftila’in Ambaliyar Ruwa da ya faru a kananan hukumomin Garko da Wudil da wasu sassa na jihar Kano.
Hassan Muhammad Shuaibu, ya ce a yanzu haka kungiyar na kan hada alkalumma na manoman da asarar ta shafa, wanda da zarar sun kammala tantance su zasu dauki matakan da suka dace don ganin anyi abin da zai taimaki manoman.
Ya kara da cewa, hauhawar farashin shinkafar da ake samu a yanzu yayi tasiri ne sakamakon halin da aka shiga na Annobar Corona, amma da zarar an girbe shinkafar ta shigo kasuwanni yawaitar ta zai sauke farashin ba da dadewa ba.
Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi, ya ruwaito cewa, kungiyar ta yi alkawarin ziyarar gani da ido a kananan hukumomin Garko da Dambatta da Albasu da Makoda da Rimin Gado da kuma Kura don don jajanta musu halin da suka samu kan su a ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!