Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sallah : Al’umma su kiyaye da wuta – hukumar kashe gobara

Published

on

Hukumar kashe gobara ta kasa ta bukaci al’ummar jihar Kano da su kiyaye sosai wajen amfani da wuta a ya yin soye-soye ko babbaka a lokacin bikin sallah.

Jami’in hurda da jama’a na hukumar a nan Kano, Nura Abdulkadir Maigida ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio inda ya nemi al’ummar Kano da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an magance afkuwar gobara a yayin bikin sallar.

Nura Maigida ya nemi al’umma da su kaucewa yin tafiya a yayin da ake ruwan sama, maimakon hakan su rika fakewa har sai ruwan ya tsagaita.

Har ila yau, Nura Mai Gida ya ce, hukumarsu ta yi shiri na musamman domin bai wa al’umma gudummuwa a duk lokacin da aka samu afkuwar gobara ko wani hatsari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!