Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Al’umma sun bukaci kotu ta rufe wani gidan kallo a Kano

Published

on

Babbar kotun shari’ar Musulinci da ke Kofar Kudu ta fara sauraron karar wasu mutane da suke neman kotu ta rufe wani gidan kallon kwallo da wajen taron biki a karamar hukumar Dala dake Kano saboda tsoran tabarbarewar tarbiyyar ‘ya’yansu.

Imran Ahmad wanda yake jagorantar masu kara ya ce tun a baya sun rubuta takaddun korafi ga hukumomin da su ka dace domin a dauki mataki kan takura musu da a keyi tare da yi musu sulhu amma suka saba.

A cewar lauyan wanda ake kara Bashir Ibrahim, ya ce, tunda fari hukumomi na gwamnati ne suka basu damar bude wadannan gurare kuma babu wata cutarwa a game da bude guraren baki daya.

Lauyan ya kuma shaidawa Kotu cewa sunje gurare da dama ciki hadda guraren da aka basu umarnin gina gidan kallan kuma anyi musu masalaha cewa ga iyakar muryar da zasuyi amfani dasu saboda kada su takurawa makotan wajen.

Haka zalika, mai shari’a Sarki Yola ya bada umarnin rubata takadda zuwa hukumin da sukayi musu sulhun domin a bai wa kotu kafin takaddun, kuma ya sanya ranar 1 ga watan 6 a 2021 domin cigaba da shari’ar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!