Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Iyaye su tabbatar da yin gwajin kwaya ga mai neman auren ’yar su – Buba Marwa

Published

on

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa Burgediya janar Buba Marwa mai ritaya, ya shawaci iyaye da su rika umartar duk wanda ya zo neman auren ‘yarsu da ya gabatar da takardar shaida da za ta nuna cewa ba ya ta’ammali da miyagun kwayoyi.

A cewar sa hakan zai taimaka gaya wajen rage matsalar shaye-shaye tsakanin matasa, ba ya ga taimakawa tattalin arzikin kasar nan.

Tsohon gwamnan mulkin soji na jihar Lagos din ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ma’aikatar shari’a ta jihar Ekiti ta shirya a birnin Ado Ekiti.

Burgediya janar Buba Marwa mai ritaya ya kuma bayyana damuwarsa karara kan yadda ya ce al’ummar kasar nan ke ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!