Labarai
Al’ummar Tudun Murtala sun koka
Gidauniyar cigaban Al’ummar unguwar Tudun Murtala sun yi kira da gwamnatin jihar Kano da ta kawo musu dauki akan hanyar su ta Tudun Murtala sakamakon lalacewar da hanyar tayi.
Shugaban gidauniyar Alhaji Yahaya Bagobiri yace al’ummar suna fama da matsalar hanya da matsalar rashin magudanar ruwa data tashi daga unguwar Gwagwarwa zuwa Tudun Murtala dake karamar hukumar Nassarawa.
Alhaji Yahaya Bagobiri ya bayyana hakan ne a ya yin taron da gidauniyar ta shirya don taya murna ga Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan na jami’ar Al’qalam bisa zama Farfesa da yayi.
Labarai masu alaka:
Wasu ‘yan kasuwar Sabon gari sun koka kan yunkurin Uba Zubairu
Inda Ranka: ‘Yan kasuwa sun koka kan biyan harajin wuta mai hasken rana a Kano
Ya ce Sheikh Abdullah Saleh Pakistan ya dade yana bada gudunmuwar ilimin addinin Islama dana zamani a unguwar Tudun Murtala wanda hakan yasa al’ummar unguwar ba zasu taba mantawa da shi ba.
Da yake nasa jawabin a yayin taron Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan bayyana farin cikin sa ya yi bisa karramawar da jami’ar Al’qalam tayi masa da gidauniyar unguwar Tudun Murtala da sauran al’ummar unguwar baki daya.
Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa al’ummar unguwar sun kira ga masu kudin unguwar da su yi koyi da Sheikh Pakistan kan irin abin da yake yiwa al’ummarsa.