Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ambaliyar ruwa: Mutane 13 sun rasa rayukan su a Bauchi

Published

on

Adadin waɗanda suka rasa rayukan su sanadiyyar ambaliyar ruwa a jihar Bauchi ya ƙaru zuwa mutane 13.

Alkaluman da aka fitar a farko ya nuna cewa, mutane biyar ne suka rasa ran su a ƙaramar hukumar Jama’are sakamakon ambaliyar ruwan, sai mutane 24 da suka samu raunuka a ƙananan hukumomi 18 na jihar.

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ta ce, a ƙaramar hukumar jama’are mutane biyar ne suka rasu, sai mutane uku a ƙaramar hukumar Gamawa, sai Ningi mutane uku yayin da mutum ɗaya a Toro ɗaya a Darazo.

Hukumar ta SEMA ta ce, ambaliyar ruwan ya shafe gidaje sama da dubu ɗaya da ɗari shida, sai kuma gonaki sama da dubu biyar da ruwan ya shafe amfanin gonar su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!