Labarai
Ambaliyar ruwa ya janyo asara ga manoman shinkafa – Kungiya
Shugaban hadaddiyar kungiyar manoman shinkafa ta kasa reshen jihar Kano ya bayyana ambaliyar ruwa da ake samu a damunar bana da cewa shi ne ya janyo tashin farashin shinkafa da ake samu a wannan lokaci baya ga matsalar rufe boda.
Alhaji Abubakar Haruna Aliyu ne ya ya bayyana hakan ta cikin shirin Baqrka da Hantsi nan a tashar Freedom rediyo da ya mayar da hanakali kan batun tashin farashin shinkafa.
Ya ce, matsalar noman shinkafa da yadda ruwan fadama ke yin ambaliya na daga cikin halin da manoma suka tsinci kan su a ciki ta yadda ya janyo tashin farashin duk da cewa an samu Karin darajar noman shinkafa a kasar nan.
Ya kuma ce babban abinda ke kara hauhawar farashin shinkafa a kasarnan bai wuce yadda wasu ‘yan kasuuwa ke boye kaya har sai sun yi tsada su fito da su.
Alhaji Abubakar Haruna Aliyu, ya ce kowanne manomin shinkafa zai iya samun tallafin bashin noma don gudanar da noman sa cikin sauki
You must be logged in to post a comment Login