Labarai
Ambaliyar ruwa yayi sanadiyar tashin manoma daga gonakinsu a Adamawa
Manoma a karamar hukumar Ganye dake a Jihar Adamawa sun koka dangane da yadda ambaliyar ruwan Daya sakko daga dutse, ya Kuma taho da yashi ya rufe musu gonakinsu.
Daya daga cikin manoman da wannan matsalar ta shafar ya shaidawa freedom Radio cewa ‘ambaliyar ruwan ta shafi gonakin ba addadi, Wanda zai iya haifarda koma baya a bangaren noma a yankin, dama wasu bangarorin kasar nan’.
Manomin ya ce ‘ko a gonarsa kadai Yana iya noman wake buhu goma, na masara goma, sai dai kuma bayan wannan matsalar ta auku bashi da damar yin hakan’.
A don haka manoman suka bayyana cewa idan har ba’a samarwa ruwan tsayayyiyar hanyar wucewa daga kan Dutsen zuwa kogi ba, to shakka babu basu da masaniya Kan irin matsalar da zasu tsinci kansu a nan gaba, duba da cewa har yanzu a cikin damunar ake.
Rahoton: Nuraddin Usman Ganye
You must be logged in to post a comment Login