Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Amurka ta cire Najeriya a cikin ƙasashen da suke hana damar yin Addini

Published

on

Amurka ta cire Najeriya daga cikin jerin ƙasashe masu hana damar yin addini.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Tun da fari dai ƙasar Amurka a shekarar 2020 ta sanya Najeriya da wasu kasashe shida cikin jerin kasashen da suke hana da suke hana damar yin Addini.

Blinken ya ce, a shekarar 2021 Najeriya ba ta cikin jerin kasashen da aka sanya waɗanda suke hana damar yin addini.

Blinken, wanda a halin yanzu yake ƙasar Kenya ta Gabashin Afrika domin ziyarar aiki, ana sa ran zai ziyarci Najeriya cikin makon da muke ciki inda zai gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da sauran mambobin majalisarsa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!